IQNA

22:52 - July 02, 2020
Lambar Labari: 3484945

Kiran Sallah Daga Burj Khalifa Dubai

Tehran (IQNA) an saka kiran salla daga dogon beni na Burj Khalifa a Dubai a matsayin alamar bude masallatai.

Kiran Sallah Daga Burj Khalifa Dubai

Shafin akhbar.net ya bayar da rahoton cewa, an saka kiran sallan ne daga dogon beni na Burj Khalifa da ke birnin Dubai a matsayin alamar bude masallatai a birnin.

Tun bayan bullar cutar corona dai aka rufe  masallatai tare da hana gudanar da sallar jam’I, inda a halin yanzu aka bayar da damar bude masallatan amma bisa kiyaye sharuddan kiwon lafiya da aka gindaya.

 

3908278

 

captcha