IQNA

Nasihar Sayyid Nasrullah Dangane Da Corona

20:08 - July 26, 2020
Lambar Labari: 3485022
Tehran (IQNA) babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Nasrullah ya yi kira ga jama’a da su kiyaye ka’idojin da hukumomin kiwon lafiya suka saka kan corona.

A zantawarsa da gidan radiyon Nur, Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, idan muka kiyaye dukkanin ka’idoji da hukumomin kiwon lafiya suka saka domin kare kai daga kamuwa da cutar corona, da kuma kauce wa yada wa wasu ita, to za mu yi nasara a wannan yaki.

A cikin sakonsa ya gabatar a cikin wani kajeren faifan bidiyo, Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, idan muka yi sakaci ko rashin kula da ka’idojin da jami’an kiwon lafiya suke sanarwa, to za a iya shiga cikin mawuyacin hali Allah ya kare mu.

Daga karshe Sayyid Nasrullah ya kirayi jama’a da su ci gaba da yin addu’a da kuma dogaro da Allah da kuma kiyayewa, domin samun saukin wannan lamari, tare da fatan Allah ya kawo karshen wannan cuta a duniya baki daya.

 

3912380

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha