IQNA

22:50 - August 16, 2020
Lambar Labari: 3485093
Tehran (IQNA) dubban yahudawa ne suke ci gaba da gudanar da zanga-zanga a cikin birnin quds domin nuna adawa da gwamnatin Netanyahu.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, dubban yahudawan sahyuniya ne suke ci gaba da gudanar da zanga-zanga a cikin birnin quds domin nuna adawa da gwamnatin Benjamin Netanyahu tare da yin kira gare shi da ya yi murabus.

Rahoton ya ce yahudawan suna rera taken cewa, Netanyahu mabarnaci ne mai cin hanci da rashawa, wanda ya jefa rayuwar yahudawa da dama cikin matsala.

A kan haka suke kira a gare shi da gwamnatinsa su yi murabus a nan take, tare daga kwalaye da aka yi rubutu a kansu da harsunan ibraniyanci da kuma turancin Ingilishi da ke bayyana shi a matsayin mai laifi.

Tun kimanin watanni uku da suka gabata ne dai yahudawan suka fara gudanar da zanga-zangar la’antar Netanyahu, wanda suke kallonsa  a matsayin mai cin amanarsu tare da handame kudadensu.

 

3916877

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: