IQNA

An Kafa Dokar Hana Shiga Birnin Karbala Har Zuwa Bayan Ashura

22:47 - August 23, 2020
Lambar Labari: 3485113
Tehran (IQNA) an kafa dokar hana shiga birnin karbala na kasar Iraki har zuwa bayan Ashura.

Tashar Bagdad Yaum ta bayar da rahoton cewa, Ala Alghanimi kakakin rundunar ‘yan sanda ta lardin Karbala ya bayyana cewa, bisa la’akari da halin da ake ciki na yaduwar cutar corona, an kafa dokar hana shiga cikin birnin karbala daga nan har zuwa ranar 13 ga watan Muharram.

Ya ce jami’an ‘yan sanda tare da jami’an kiwon lafiya na cibiyar yaki da corona ta kasa, za su ci gaba da yin aiki tare domin tabbatar da cewa ba a samu wadanda suka karya wanann doka ba.

Inda ya cea  halin yanzu ‘yan asalin garin na Karbala ne kawai ake baiwa damar su shiga cikin garin, amma ba a barin wani daga waniu gari na Iraki ko daga wata kasar su shiga birnin, domin kaucewa gudanar da tarukan da za su hada mutane da yawa.

Yanzu haka dai adadain wadanda suka kamu da cutar corona a kasar Iraki ya kai mutane dubu 200, yayin da wadanda suka rasa rayukansu kuam adadinsu ya kai dubu 6.

 

3918502

 

captcha