IQNA

An Wanke Dakin Ka'abah Mai Alfama

22:30 - September 04, 2020
Lambar Labari: 3485148
Tehran (IQNA) an gudanar da taron wanke dakin Ka'aba mai alfama tare da halartar sakin Makka.

Shafin yada labarai na Alkhalij Today ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da taron wanke dakin Ka'aba mai alfama tare da halartar sakin Makka Khalid Faisal, wanda ya wakilci sarkin kasar ta Saudiyya.

An dauki kwararan matakai na kiwon lafiya a wurin, inda Khalid Faisal ya yi amfani da ruwan zamzam da kuma ruwan wardi ya wanke bangon dakin Ka'aba.

Sheikh Abdulrahman Sudais mai kula da haramin makka da madina, tare da wasu daga cikin malaman kasar gami da jami'ai, sun halarci wurin.

برگزاری مراسم شستشوی کعبه با حضور امیر مکه
 
برگزاری مراسم شستشوی کعبه با حضور امیر مکه
 
برگزاری مراسم شستشوی کعبه با حضور امیر مکه
 

3920785

 

captcha