IQNA

Ganawa Tsakanin Nasrullah Da Haniyya

22:52 - September 06, 2020
Lambar Labari: 3485154
Tehran (IQNA) babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya gana da shugaban kungiyar Hamas Isma’il Haniyya.

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah, ya karbi bakuncin Shugaban kungiyar Hamas ta palasdinu tare da mataimakinsa Salih al-Arury da kuma tawagar da take yi masa rakiya, inda bangarorin biyu su ka tattauna halin da ake ciki ta fuskokin siaysa da tsaro a Palasdinu da Lebanon da kuma cikin yankin gabas ta tsakiya.

Har ila yau bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin da za a kalubalanci ‘yarjejeniyar karni da sauran hatsuruka da suke yi wa batun Palasdinu barazana kamar kulla alakar da kasashen larabawa su ke yi da Isra’ila.

Wani batu muhimmanci da kungiyoyin na gwagwarmaya su ka tattauna shi ne ci da yin tsayin daka akan tafarkin gwagwarmaya da jajircewa duk wani matsin lamba da makiya suke yi musu.

Kungiyoyin Hizbullah da Hamas sun kuma jaddada karfada alakar da take a tsakaninsu ta imani da ‘yan’uwantaka da jihadi da makoma guda, haka nan kuma bunkasa hanyoyin aiki tare a tsakaninsu.

 

3921130

 

 

 

 

 

 

captcha