IQNA

Za A Bude Masallatai A Kasar Libya

22:29 - October 07, 2020
Lambar Labari: 3485255
Tehran (IQNA) mahukunta a kasar Libya sun sanar da cewa za a bude masallatai a fadin kasar daga ranar Juma’a mai zuwa.

Shafin yada labarain Libya Obsever ya bayar da rahoton cewa, ma;aikatar kula da harkokin addini ta kasar Libya ta sanar da cewa, daga wannan Juma’a mai zuwa mahukunta a kasar Libya sun sanar da cewa za a bude masallatai a fadin kasar.

Wannan bayani na zuwa bayan shafe tsawon watanni bakawai masallatai suna rufe a fadin kasar saboda yaduwar cutar corona, inda a halin yanzu aka yanke shawarar bude masallatan.

Bayanin ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar da cewa, an dauki waan mataki bayan yin shawara tsakaninta da hukumar yaki da cutar corona, inda aka cimma matsaya kan bude masallatan.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, za  abude masallatan ne bisa wasu sharudda, da suka hada da kiyaye dukkanin kaidojin da aka gindaya domin hada yaduwar cutar, kamar yadda kuma hukumomin kiwon lafiya za su yi iyakacin kokarinsu a wanna fage.

3927829

 

 

captcha