IQNA

Kasashe 47 Ke Halartar Taron Makon Hadin Kai

22:13 - October 29, 2020
Lambar Labari: 3485318
Tehran (IQNA) Da safiyar yau Alhamis ne aka bude taron makon hadin kan al’ummar musulmi na duniya karo na talatin da hudu a birnin Tehran na kasar Iran.

Da safiyar yau Alhamis ne aka bude taron makon hadin kan al’ummar musulmi na duniya karo na talatin da hudu a birnin Tehran don tunawa da zagayowar ranar da aka haifi Manzon Allah (s.a.w.a) a bisa wasu riwayoyin, wanda kuma za a dau kwanaki biyar har zuwa ranar 17 ga watan Rabiul Awwal ana yinsa.

An bude taron na bana ne dai wanda saboda yahuwar cutar nan ta Coronavirus ya sa za a gudanar da shi ne ta hanyar bidiyo daga nesa, da jawabin da Ayatullah Nasir Makarem Shirazi, daya daga cikin maraja’an duniyar Shi’a da ke birnin Qum na Iran da kuma jawabin shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baƙir Qalibaf wadanda duk suna gudanar da jawaban na su daga nesa.

Bisa sanarwar da wadanda suka shirya taro suka fitar, kimanin malamai da masana da masu fadi a ji 167 daga kasashe 47 na duniya ne za su halacci tarurrukan da za a gudanar tsawon wadannan ranaku da kuma gabatar da jawabansu kan hadin kan al’ummar musulmi da sauran lamurran da suka shafi musulmin.

Shi dai wannan taron ana gudanar da shi ne a kowace shekara daga ranar 12 ga watan Rabiul Awwal zuwa ranar 17 ga watan Rabiul Awwal da dukkanin musulmi suka yi ittifaki kan daya daga cikin wadannan ranaku biyun ne aka haifi Manzon Allah (s.a.w.a), don haka ne marigayi Imam Khomeini (r.a) ya sanya wadannan ranaku sunan ranakun makon hadin kai inda masana da malamai da jagororin duniyar musulmi suke taruwa don tattauna batutuwan da suka shafi duniyar musulmin.

 

3931975

 

 

captcha