IQNA

23:50 - November 11, 2020
Lambar Labari: 3485356
Tehran (IQNA) wani abu mai fashewa da aka dasa a makabartar da ba ta musulmi ba a birnin Jidda na Saudiyya, ya fashe.

A yau Laraba ne dai wani abu mai fashewa da aka dasa a makabartar da ba ta musulmi ba a birnin Jidda na Saudiyya, ya fashe inda ya yi wa wasu mutane da dama rauni.

Kakakin fadar gwamnatin gundumar Makka mai alfarma ya shaida wa manema labaru cewa; Jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike akan harin da aka kai a yayin da karamin jakadan kasar Faransa ya halarci makabartar.

Sultan al-Dusary ya kara da cewa; Wani ma’aikacin karamin ofishin jakadancin Girka da wani jami’in tsaron Saudiyya sun jikkata.

A can birnin Paris kuwa, ma’aikatar harkokin wajen Faransa ce ta sanar da cewa; Nakiyar ta tashi ne a lokacin da ake gudanar da kwarya-kwaryar bikin tunawa da yarjejeniyar tsagaita wutar yakin duniya na farko a ranar 11 ga watan Nuwamba na dubu daya da dari tara da sha takwas.

 

3934713

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: birnin Jidda ، saudiyya ، Nakiya ، faransa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: