IQNA

22:49 - November 17, 2020
Lambar Labari: 3485374
Tehran (IQNA) Ragib Musataf Galwash fitaccen makarancin kur’ani ya rasu a 2016 yana da shekaru 78.

Ragib Mustafa Galwash wanda an haife shi ne a  ranar 5 ga watan Yuli 1938 a Masar, ya rasu a ranar 4 ga Fabrairun 2016, ya kasance daya daga cikin fitattun makaranta kur’ani a kasar Masar, wanda kuma ya shahara a duniya, inda ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya da dama, da suka hada da Faransa, Amurka, Canada, Burtaniya, Iran da sauransu.

Mustafa Galwash ya tafi Iran har sau 4, inda ya halarci taruka daban-daban, kuma ya gana da jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei a lokutan ziyararsa  akasar ta Iran.

A cikin wanann hotun bidiyon za ku iya ganinsa a wani taro a husainiyar Imam Khomeini (RA) shekaru 31 da suka gabata.

 

3935774

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: