Yau ne daren Juma'a na farko a cikin wannan wata na Rajan mai alfarma, wanda Allaj madakakin sarki yake ninka lada ga masu ayyukan ibada a cikinsa.
Wanann dare baya ga kasancewarsa daren Juma'a ne, haka nan kuma dare ne mai albarka bisa karin albarka, domin kuwa shi ne daren Juma'a na farko a cikin wanann wata na Rajab mai albarka.
Manzon Allah (SAW) ya kwadaitar matuka dangane da yin ibada da ambaton Allah madaukakin sarki a cikin wannan dare mai albarka, kamar yadda kuma addu'oi da dama sun zo da ake a cikin wannan dare.
Ya zo daga cikin ayyukan wannan dare, salla raka'a 12, kowace raka'a ana karanta suratul Hamd kafa daya, sai kuma aka karanta surat Qadr kafa 3 da kuma surat tauhid kafa 12, ana yin salla tsakanin kowace raka'a biyu.
Bayan kammalawa sai a yi salati ga manzon Allah da alayensa kafa 70, bayan nan sai a yi sujada a karanta sau 70 (Subbuhun Quddusun Rabbul Mala'ikati Warruh) sai kuma a dago daga sujadar a karanta sau 70 (Rabbi Igfir warham wa tajawaz amma ta'alam innaka antal Aliyul A'azam) sannan sai a yi addu'a da izinin Allah za a samu biyan bukata.
Ya zo a cikin ruwayoyi da dama kan cewa, duk wanda ya yi wannan salla, Allah madaukakin sarki da ikonsa da rahamarsa zai gafarta masa zunubbansa baki daya.