IQNA

An Karyata Labarin Cewa Ayatollah Sistani Ya Kamu Da Corona

21:32 - February 27, 2021
Lambar Labari: 3485695
Tehran (IQNA) an karyata labarin da ke cewa Ayatollah Sistani ya kamu da cutar corona.

Shafin yada labarai na Mawazin News ya bayar da rahoton cewa, ofishin babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya karyata labarin cewa, malmin ya kamu da cutar corona.

Bayanin ya ce babu gaskiya a wannan labari, kuma malamin yana cikin koshin lafiya, yana gudanar da harkokinsa kamar yadda ya saba.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa Hojjatol Islam Ahmad Safi wakilin Ayatollah Sistani ya kamu da cutar ta corona, kamar yadd majiyoyin asibiti ma sun tabbatar da hakan, amma yana ci gaba da karbar magani.

3956475

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :