IQNA

Baje Kolin Kwafin Kur'anai Rubutun Hannu A UAE

23:57 - May 23, 2021
Lambar Labari: 3485943
Tehran (IQNA) an nuna kwafin kur'anai da aka rubuta da hannu a baje kolin kur'ani a kasar UAE.

Shafin yada labarai na jaridar Alkhalij ya bayar da rahoton cewa, dakin karatu na Kalba a yankin Sharijah a hadaddiyar daular larabawa ya bude wani baje kolin kur'anai rubutun hannu.

A wannan baje kolin kur'anai  ana nuna wasu kwafin kur'anai da aka rubuta daruruwan shekaru da suka gabata a cikin tsarin rubutu mai kyau mai kayatarwa.

Rahoton ya ce a wurin ana nuna kwafin kur'anai kimanin guda 40, wadanda mafi yawansu an rubuta su ne a lokacin daular Usmaniya ta Turkawa, wato daruruwan shekaru ad suka gabata.

Alhimadi shi ne shugaban baje kolin, ya kuma bayyana cewa, an samo wadannan kwafin kur'anai ne daga kasashe daban-daban, inda aka tara su wuri guda domin nuna su a wannan baje koli, wanda yake samun mahalarta daga ciki ciki da wajen kasar.

 

3973118

 

captcha