IQNA

Jami’an Tsaron Yahudawa Sun Ci Gaba Da Kai Farmaki Kan Masallacin Quds

22:10 - May 25, 2021
Lambar Labari: 3485947
Tehran (IQNA) Jami’an tsaron gwamnatin yahudawan Sahyuniya sun sake kaddamar da farmaki a kan masallacin Quds mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya jami’an tsaron yahudawan Isra’ila sun kaddamar da farmaki a kan masallacin Quds, da kuma kan Falastinawa mazauna birnin na Quds, inda suke bi gida-gida suna kama jama’a.

Rahoton ya ce, yahudawan sun auka kan masallata a cikin masallacin tare da antaya hayaki mai sanya hawaye a kan masallata.

Baya ga haka kuma jami’an tsaron yahudawa suna ci gaba da bi gida-gida suna kama Falastinawa suna yin awon gaba da su, musamman ma dai matasa.

Wannan mataki na zuwa ne bayan cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimmawa, wanda kuma daga cikin sharuddan Hamas da sauran kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa, har da dakatar da duk wani shishigi na Isra’ila a kan masallacin Quds, da kuma Falastinawa mazauna birnin, wanda hakan ke nufin cewa Isra’ila ta yi falali da wannan yarjejeniya.

Sai dai a nata bangaren kungiyar Hamas ta yi gargadin cewa, ci gaba da keta alfarmar masallacin Quds da Isra’ila ke yi, ba a bu ne da za a zura ido a kansa ba, domin kuwa hakan yana a matsayin keta alfarmar addinin muslunci ne da ma dukkanin msuulmi a duniya.

Wannan yana zuwa a kan da’awar da yahudawan sahyuniya suke yi kan cewa masallacin Aqsa nasu ne, amma babban malamin cibiyar ilimi ta Azhar da ke Masar ya mayar musu da martani tare da ba su cikakkiyar amsa da ke rusa da’awar tasu.

3973590

 

captcha