IQNA

Firayi Ministan Iraki: Dakarun Hashd Al-shaabi Ne Suka Karya Lagon 'Yan Ta'addan Daesh

19:54 - June 26, 2021
Lambar Labari: 3486051
Tehran (IQNA) Ana gudanar da bukukuwan cikar shekaru 7 da kafa dakarun al’ummar kasar Iraki na Hashd al-shaabi.

Shafin yada labarai na alaha ya bayar da rahoton cewa, a yau ne ake gudanar da bukukuwan cikar shekaru 7 da kafa dakarun al’ummar kasar Iraki na Hashd al-shaabi, bayan da shugaban addini na kasar Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya bayar da fatawar kafa rundunar sa-kai ta al’umma domin fatattakar ‘yan Daesh, a alokacin da suke hankoron mamaye kasar.

Dakarun Hashd Al-shaabi sun gudanar da fareti a yau tare da nuna wasu daga cikin kayayyakinsu na yaki, kamar yadda kuma manyan kwamandojin rundunar gami da manyan jami’an tsaro da kuma jami’an gwamnati duk sun halarci wurin.

Firayi ministan kasar Iraki Mustafa Alkazimi na daga wadanda suka halarci taron fareti na dakarun Hashd Al-sha’aabi, inda kuma ya gabatar da jawabi a wurin, tare da tabbatar da cewa dakarun Hashd Al-shaabi ne suka taka muhimmiyar rawa wajen fatattakar ‘yan ta’addan Daesh daga Iraki, kuma har yanzu akwai sauran aiki a gabansu, domin kuwa ‘yan ta’addan suna nan, rauni ne kawai suka yi.

Duk da cewa wadanda suka kafa rundunar Hashd Al-shaabi mabiya mazhabar shi'a ne a Iraki, amma kuma a lokaci guda rundunar ta hada dukkanin bangarorin al'ummar kasar, da suka hada da 'yan sunnah, kiristoci, Izidiyawa, Turkaman, kurdawa da sauransu.

A cikin shekarar 2014 ne dubban mayakan ‘yan ta’adda daga kasashen duniya daban-daban suka shiga cikin kasar Iraki ta kan iyakokin kasashen larabawa da suke makwabtaka da kasar, inda suka mamaye wasu yankuna a arewacin Iraki, amma bayan fatawar Ayatollah Sistani, an kafa rundunar Hashd Al-shaabi, wadda marigayi Kasim Sulaimani ya bayar da gudunmawa wajen kafa ta, kuma su ne suka kawo ragargaza ‘yan ta’addan na Daesha Iraki.

 

3980062

 

captcha