IQNA

23:03 - July 29, 2021
Lambar Labari: 3486151
Tehran (IQNA) an gudanar da tarukan ranar Idin Ghadir a yankunan gabashin kasar Saudiyya.

Shafin yada labarai na Aljuhainah ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da tarukan ranar Idin Ghadir a garin Qatif da ke gabashin kasar Saudiyya.

Wannan taro dai yana daga cikin muhimman taruka da mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) suke gudanarwa a ko'ina a cikin fadin duniya, domin tunawa da ranar jawabin karshe da manzon Allah (SAW) ya yi bayan kammala aikin hajjin bankwana.

A bisa ruwayoyi da sahabbai 115 suka ruwaito wanda hakan yasa ruwayar ta zama a matsayin tawatur saboda ingancinta,a  ranar ne Manzon Allah (SAW) ya bayyana dan uwansa kuma surukinsa kuma sahabinsa Imam Ali (AS) a matsayin majibincin lamarin muminai a bayansa.

Mabiya mazhabar Ahlul bait a kasar Saudiyya wadanda su ne kashi 15 na al'ummar kasar suna gudanar da irin wadannan taruka na tunawa da wannan rana a yankunansu da suke gabashin kasar.

 

3987221

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar Saudiyya ، taruka ، idin ghadir ، muminai ، majibincin lamarin
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: