Shafin jaridar Ala'in ya bayar da rahoton cewa, an fara aiwatar da wannan shiri ne na koyar da kurame karatun kur'ani mai tsarki ta hanyar karatun ishara a birnin Aden da ke kudancin kasar Yemen.
An fara gudanar da shirin ne a wata makarantar kurame, inda ake koyar da su amma ta hanyar karatun ishara, inda a halin yanzu an sanya karatun kur'ani ya zama daya daga cikin abubuwan da za a rika koyar da su.
Da farko dai an fara da mutane 30, da suka hada da malaman makarantar su 10 sai kuam wasu dalibai 20 daga cikin dalibai masu hazaka.
Iman Hashem ita shugabar wannan shiri, ta bayyana cewa a halin yanzu an samar da littafi wanda yake dauke surorin kur'ani wanda aka rubuta shi da rubutun ishara, wanda da shi ne za a rika koyar da kurame.