A rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, Anas Burraq fitaccen makarancin kur'ani mai tsarki ne dan kasar Morocco wanda ya shahara a wannan fage an karatu da hardar kur'ani.
Shi ne ya zo na uku a gasar karatun kur'ani ta duniya da aka gudanar karo na bakawai a birnin Shajah na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a shekara ta 2014.
baya ga nan , ya ziyarci kasashen duniya da dama daban-daban domin yin karatun kur'ani a taruka na addini, daga cikin har da kasar Italiya.
A cikin wannan faifan bidiyo ya karanta ayoyi na 75 zuwa 89 a cikin surat Shu'ara kamar dai yadda za a iya gani da saurare idan aka matsa: