Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, an kai harin ta'addanci ne a yau a kan wani masallacin Juma'a a Lardin Kunduz na kasar Afghanistan a lokacin da ake sallar Juma'a, kuma mutane da dama suka rasa rayukansu da kuma jikkata.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, wani dan ta'adda ne da ya yi jigidar bama-bamai ya tarwatsa kansa a tsakiyar masallata a lokacin sallar Juma'a a masallacin mabiya mazhabar Ahlul bait a yankin Khan Abad da ke cikin gudumar Kunduz.
Mai magana da yawun kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya fitar da bayani da ke cewa, wasu 'yan ta'adda sun kai wa 'yan uwanmu musulmi hari a lokacin sallar Juma'a, kuma wasu da dama sun yi shahada wasu kuma sun jikkata.
Ya zuwa yanzu dai akalla mutane 100 ne aka tabbatar da rasuwarsu yayin da kuma wasu fiye da 200 suka samu munanan raunuka.
Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma dai ana kyautata zaton cewa kungiyar 'yan ta'addan Daesh ce take da hannu a wannan hari.