
Yayin da yake magana a taron birnin Manama a babban birnin Bahrain, Fouad Hussein ya ce: Bisa la'akari da tambayoyin da ake yi kan ko Iraki za ta shiga cikin yarjejeniyar kulla alaka da Isra’ila, amsar ita ce a'a.
Ministan na Iraki ya kara da cewa: “Akwai dalilai da yawa kan hakan, amma ba zan yi bayani a nan ba”. Wannan abu ne mai wahala kuma ba zai faru da Iraki ba.
A farkon watan Oktoba, wani ministan Isra'ila ya yi hasashen cewa Iraki za ta kasance daya daga cikin kasashen da za su daidaita dangantakarsu da Isra'ila da ma wasu daga cikin kasashen larabawa da na musulmi.
Bugu da kari kan hakan, ministan ya tabbatar da cewa akwai fahimta da tuntubar juna kai tsaye tsakaninsu da kasar Saudiyya, da kuma wasu daga cikin kasashen yankin tekun Farisa.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar "Abraham" a watan Satumban 2020 domin daidaita dangantaka tsakanin gwamnatin yahudawan Sahayoniya, da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain a karkashin kulawar Washington, sannan daga bisani kasashen Morocco da Sudan suka biyo baya.
https://iqna.ir/fa/news/4014785