Kamfanin dilalncin labaran iqna daga kasar Iraki ya bayar da rahoton cewa, za a fara baje kolin ne a ranar gobe Laraba 29 ga watan Disamba 2021 a filin wasanni na Kirkuk da ke kan titin Bagadaza, kuma za a ci gaba da shi har zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2022.
Cibiyoyin al'adu da hukumar wayar da kan al'ummar Iraki (North Axis Command) za su hada kai wajen gudanar da wannan baje kolin, wanda zai kunshi bangarori daban-daban da suka hada da baje kolin ayyukan kur'ani, littafai, nuna na'urorin dijital, nano, sana'o'in hannu da yara da matasa suke samarwa.
Za a bude wannan baje kolin ne tare da halartar manyan jami'an kasar Iraki da jami'an yankin a birnin Kirkuk, kuma an gayyaci 'yan kasar ta Iraki da su halarta.