IQNA

Yahudawa Sun Kutsa Kai Cikin Masallacin Quds Domin Tarukan Tilmud

22:27 - December 28, 2021
Lambar Labari: 3486743
Tehran (IQNA) A safiyar yau talata ‘yan sahayoniya ‘yan kaka gida sun shiga masallacin Al-Aqsa ba bisa ka’ida ba domin gudanar da ibadar Tilmud na addinin yahudanci.

Rahotanni sun ce, Jami'an 'yan sandan gwamnatin sahyoniyawan sun kutsa kai cikin masallacin Al-Aqsa daga Bab al-Magharbeh domin nuna goyon bayansu ga 'yan sahayoniyawan a safiyar yau ranar Talata 27 ga watan Disamba.

Dakarun ‘yan sandan yahudawan sahyoniya da sauran yahudawan sun yi maci a harabar masallacin Al-Aqsa inda suka gudanar da ibadar Talmud na Yahudawa a kusa da Bab al-Rahma da ke gabashin masallacin mai alfarma.

Yahudawan sahyoniyawan 'yan mamaya na ci gaba da kai hare-hare akai-akai a masallacin Al-Aqsa.

Bisa  ga yadda dokokin kasa da kasa na majalisar dinkin duniya suka tanada, ofishin kula da bayar da agaji na birnin Quds da ma'aikatun kasar Jordan ne kawai  a hukumance ke da hakkin bayar da izinin shiga wuraren ibadar musulmi idan har akwai bukatar hakan, amma yahudawa suna yin gaban kansu a  duk lokacin da suka ga dama.

4024173

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yahudawa ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha