IQNA

Tarjamar Kur'ani A Cikin harsuna 43 Na Duniya A Masar

22:52 - January 23, 2022
Lambar Labari: 3486857
Tehran (IQNA) Ministan ma'aikatar kula da harkokin addini a masar ya ce kawo yanzu kasar ta fassara kur'ani mai tsarki zuwa harsuna 43.

Ministan ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar Mohammed Mukhtar Juma ya sanar da cewa, ma'aikatar tana jagorantar ayyukan tarjama daga harshen larabci zuwa wasu harsuna domin tabbatar da cewa tafsirin kur'ani mai tsarki ya kubuta daga gurbata da rashin fahimtar nassi.

Juma ya bayyana cewa, wannan aiki na da nufin yada al’adun muslunci ta hanyar tarjama kur’ani mai tsarki zuwa harsunan kasashen waje, inda ya kara da cewa ma’aikatar tana yin nazari sosai kan zabar mafi kyawun tafsiri domin kada a yi amfani da nassosin kur’ani bisa kura-kurai a cikin tarjamar.

Ministan kyauta na kasar Masar, ya bayyana cewa ma'aikatar ta kammala tarjamar kur'ani mai tsarki zuwa harsuna 43, ya ce: "An yi sabbin tafsirin kur'ani mai tsarki a Masar cikin harsunan Adriatic da Hausa da kuma Girkanci."

Ministan ya bayyana cewa, a zagaye na gaba na bikin baje kolin littafai na birnin Alkahira, za a gudanar da wani taron karawa juna sani kan yadda za a samu taimako daga kwararrun masana harshen larabci da masu fassarar harsunan kasashen waje, wajen tarjama kur'ani.

 

4030764

 

 

captcha