IQNA

An kashe mutane da dama a kasar Saudiyya

23:32 - March 13, 2022
Lambar Labari: 3487048
Tehran (IQNA) Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta sanar da aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutane da dama saboda dalilai na siyasa da banbancin mahanga da kuma imaninsu.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Sanarwar ta mahukuntan Saudiyya ta ce, wadannan mutane suna suna kai hare-hare kan wuraren ibada da wasu muhimman cibiyoyi na gwamnati wadanda ke da muhimmanci ga tattalin arzikin kasar, suna sanya idanu kan wasu jami'ai.

A cewar sanarwar, wadannan mutanen da aka yanke wa hukuncin kisa, sun nemi tada zaune tsaye da haifar da fitina da hargitsi a kasar, ko kuma zuwa wuraren da ake rikici a kasashen waje, ko kuma su aiwatar da shirin ISIL da Al-Qaeda.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta kuma yi ikirarin cewa wasu daga cikin wadannan mutane suna da alaka da kungiyar Houthi ta Yemen.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta fitar ta biyo bayan an aiwatar kisan a kan wadannan mutane da aka yanke musu hukuncin kisa da kuma tuhumar da ake musu.

Daga cikin mutane 81 da aka lissafa, akasari ‘yan kasar Saudiyya ne, 7 kuma ‘yan kasar Yemen ne, 1 kuma dan kasar Syria ne.

 

https://iqna.ir/fa/news/4042396

captcha