A yayin wannan taro ne dalibai da malaman makarantar Tebyan suka karrama shi ta hanyar yin karatun kur’ani da kuma bayani kan sifofin Ali Ramadan Al-Awsi, tare da karrama wannan mai hidima ga kur’ani.
Ali Ramazan Al-Awsi shi ne darektan makarantar Tebyan, kuma ya yi fiye da shekaru ashirin na hidimomin kimiyya da ilimantarwa a fagen koyar da kur’ani.
A cewar cibiyar muslunci ta kasar Ingila, a wannan taro, Hojjatoleslam Mehdi Jafari, bayan ya gabatar da sallar jam'i, ya yi bayani kan babban matsayi na malamin, ya kuma kara da cewa: "Bugu da kari kan ayyukan tarbiya, da'a da kuma tawali'u na Dr. Al-Awsi. , rubuce-rubucensa za su rayu har abada.” .
Idan dai ba a manta ba Ali Ramazan Al-Awsi malami ne a jami’ar kimiyyar addinin musulunci ta duniya da ke birnin Landan, kuma masanin kur’ani dan kasar Iraqi da ke zaune a kasar Birtaniya.
Al-Awsi ya kasance yana daga tutar kusantar juna a tsakanin mabiya addinan Musulunci, kuma ya sha nada shi a matsayin sakataren tarurruka na addini a kasashe daban-daban.
Littafin Manhajiyah fi Tafsireh Al-mizan, na daya daga cikin muhimman ayyukan Ali Ramadan Al-Awsi, wanda Sayyid Hossein Mirjalili ya fassara zuwa harshen Farisanci.