IQNA

Kotun Faransa ta soke rufe wani masallaci

14:35 - March 25, 2022
Lambar Labari: 3487089
Tehran (IQNA) Wata kotu a Faransa ta yi watsi da matakin da gwamnati ta dauka na rufe wani masallaci da ke kusa da birnin Bordeaux.

A wani rahoton TRT, Lauyan Masallacin Al-Farooq Sefen Guez Guez ya bayyana cewa, Kotun Gudanarwa ta Bordeaux ta soke hukuncin da ofishin Gwamnan Girond ya yanke a ranar 14 ga Maris na rufe Masallacin na tsawon watanni shida.

Ya ce hukuncin da kotun ta yanke a kan rufe masallatai wani mataki ne na rashin adalci da aka yi a shekarun baya, ya kara da cewa: “Yanzu musulmi na iya haduwa a wannan masallacin.

An rufe Masallacin Al-Farooq da ke gundumar Pasak kusa da Bordeaux bisa zargin cewa masu tsatsauran ra'ayi an amfani da wurin da sunan yada addinin Islama.

A watan Agustan da ya gabata ne dai babbar kotun kare kundin tsarin mulkin kasar Faransa ta zartar da wata doka mai cike da ce-ce-ku-ce da ta takaita ayyukan musulmi da kuma bayar da damar rufe wuraren ibadarsu da sunan ayyukan tsaro.

Majalisar dokokin Faransa ta amince da kudirin dokar a watan Yuli, duk kuwa da kakkausar suka daga bangaren wasu ‘yan siyasa dama.

Gwamnati ta yi iƙirarin cewa dokar na da nufin ƙarfafa “tsarin zaman lafiya ” na Faransa, amma masu sukar sun ce dokar ta tauye ‘yancin addini da kuma mayar da musulmi saniyar ware.

An dai soki dokar da takurawa al'ummar musulmi a kasar Faransa, Kudurin dokar ya baiwa hukumomi damar shiga a masallatai da kungiyoyin da musulmi suke gudanarwa, da kuma kula da kudaden kungiyoyin musulmi da kungiyoyi masu zaman kansu.

A cewar dokar, an kuma haramta wa marasa lafiya zabar likita bisa la’akari da jinsi saboda addini ko wasu dalilai.

Kungiyoyin kasa da kasa da na masu zaman kansu musamman ma Majalisar Dinkin Duniya sun caccaki Faransa kan yadda ta ke kai wa musulmi hari da kuma mayar da su saniyar ware ta hanyar doka.

A cewar wani rahoto da aka fitar a ranar 2 ga watan Maris, kasar Faransa ta mallaki masallatai, makarantu, kungiyoyi da wuraren aiki na musulmi kusan 25,000 tun daga watan Fabrairun 2018, tare da rufe wani adadi mai yawa daga cikinsu.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4044856

captcha