IQNA

Baje kolin rubuce-rubucen kur'ani da aka yi da hannu a Riyadh Saudiyya

16:35 - April 25, 2022
Lambar Labari: 3487212
Tehran (IQNA) An kaddamar baje kolin wasu tarin rubuce-rubucen kur'ani mai tsarki da ba a saba gani ba a dakin karatu na Sarki Abdulaziz da ke birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Saudiyya cewa, dakin karatu na sarki Abdul Aziz da ke birnin Riyadh ya kaddamar da bikin baje kolin kur’ani mai tsarki da ba a saba gani ba a yayin bikin ranar tarihi ta duniya.

Dakin karatun ne ya shirya baje kolin don taimakawa wajen gabatar da al'adun Larabawa da na Musulunci.

Dakin karatun dai na da tarin kur'ani mai tsarki, wadanda akasarinsu an rubuta su ne a tsakanin karni na goma zuwa goma sha uku bayan hijira, kuma yana dauke da kur'ani 267 da wasu kayan tarihi masu kima.

A cikin wannan ɗakin karatu, an baje kolin kur'ani na Indiya da wasu kayan tarihi iri-iri da kuma misalan kyawawan ayyukan Sinawa, Kashmiri da Mamluk.

An nuna rubutu da aka yi da haruffa daban-daban kamar su Kufi, Naskh, Thals, Timbuktu, da na Sudan , da kuma rubutun Levant, Iraki, Masar, Yemen, da Najd da Hejazi.

 

4052083

 

captcha