IQNA

Hannayen Shaidan na a rufe a watan Ramadan

19:38 - April 25, 2022
Lambar Labari: 3487214
Tehran (IQNA) Daya daga cikin abubuwan da ake fada dangane da watan Ramadan shi ne cewa an daure hannun shaidan a cikin wannan wata. Amma shin hakan yana nufin babu wanda shaidan zai iya ya jarabce shi ko ya yi kuskure a wannan watan?

A cikin hudubar Sha’abaniyya, Manzon Allah (S.A.W) ya bayyana siffofin watan Ramadan mai alfarma inda ya ce a wani bangare nasa: "Shaidanu suna daure ku roki Allah kada ya bari su doru a kanku." An ciro mas’aloli guda biyu daga wannan bangare na addu’ar Sha’abaniya; Na farko, ana takurawa shaidanu a cikin watan Ramadan; Amma batu na biyu yana nuni da cewa a lokaci guda shaidan yana iya mamaye masu azumi.

Alkur'ani ya siffanta Shaidan a matsayin mai rauni sosai kuma ya jaddada cewa Shaidan da mataimakansa ba su da iko a kan bayin Allah; a matsayin amsa ga barazanar da Shaiɗan ya yi na batar da bayi, Allah ya yi magana game da rashin ikonsa kan hakan, sai dai kawai a kan waɗanda suka bi shi.

Mallakar da aka ambata a cikin ruwayar da ta gabata ita ma tana nufin tasiri mai tsanani.

Ramadan lokaci ne mai mahimmanci don ƙarfafa ruhi. Shine watan  da aka saukar da Alkur'ani sauka ta bai daya; Daren Lailatul kadari yana cikinsa; Ibada ta bambanta a wannan watan, kamar yadda numfashin mumini da barcinsa ibada ne; Karatun aya daya daga cikin Alkur'ani daidai yake da karatun Alkur'ani baki daya. Don haka ne shaidan ba zai iya ratsa zukatan masu azumi masu ibada da ambaton Allah a kowane lokaci a cikin wannan wata ba.

Ta haka ne zukatan masu azumi ke cika da haske da ambaton Allah saboda azumtarsu da halartar watan Ramadan da ayyukan watan Ramadan mai alfarma, kuma shaidan ya mika wuya ga irin wannan zuciya domin kuwa ita irin wannan zuciya ta mika lamarinta ga Allah.

To idan mai azumi bai gina kansa ba, yana ambaton Allah a cikin wadannan kwanaki, hasken zuciyarsa zai yi rauni, kuma Shaidan zai iya yin tasiri a kansa.

A daya bangaren kuma an ruwaito cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce: Iblis yana gudana a cikin mutum kamar malalar jini, don haka ku takura magunarsa da yunwa.

captcha