IQNA

Siffofi na musamman na bakuntar watan Ramadan

21:05 - April 27, 2022
Lambar Labari: 3487224
Tehran (IQNA) Kowane bakunci  na da sharudda da halaye kuma kowace al’umma tana maraba da mutane na musamman; Ramadan kuma yanayi ne mai daraja  yanayi na musamman wanda  komai na yau da kullun, ya zama na musamman a cikinsa  Ko da numfashi ne.

A cikin lexicography, daya daga cikin ma'anar "Ramadan" shine ƙonewa, don kada ya kasance yana da hayaki da toka. Dalilin da ya sa ake kiran wannan wata da Ramadan shi ne saboda ana kona zunubban mutane  ba tare da wani ya sani ba ko  ya fahimta ba.

Watan Ramadan shi ne watan saukar Alkur’ani kuma shi ne watan da aka ambaci sunansa a cikin Alkur’ani. A cikin tafsirin hujja, an karbo daga Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Dukkanin littafan sama an saukar da su ne a cikin watan Ramadan.

A cikin Ramadan, ana gayyatar muminai zuwa liyafar ubangiji. Ya zo cikin kur’ani kan kan wajabcin azumi a cikinsa  “Ya ku wadanda suka yi imani, an wajbata azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suka gabace ku” (Al-Baqarah: 183)

Babban abin da ke cikin wannan liyafa ta Ramadan shi ne Allah ne mai masaukin baki kuma shi da kansa ya gayyace su.

Hanyar karbar wannan gayyata  ita ce addu'a, karatun kur’ani, tuba da istigfari da zikirin Allah madaukakin sarki.

Lokacin liyafar kuma shi ne watan Ramadan, wanda ruwayoyi suka zo, na farkonsa rahama ne, tsakiyarsa gafara, kuma karshensa lada ne.

Abincin wannan wata shine abincin ruhi  wanda ya zama dole don haɓaka ruhi , ba abincin jiki ban a yau da kullum da aka saba da shi. Babban jigon aikin ibada a cikin wannan liyafa shine karatun ayoyin alqur'ani

Sharudda da za su sanya azumi ya yi armashi kuma ruhi ya karfafa sun hada da   nisantar halaye da sifofi kamar karya, zunubi, sabani, hassada, tsegumi, adawa da gaskiya, zagi da zargi da fushi,  zalunci da cin mutuncin mutane, gafala, cudanya da fasikai, da kuma  haramcin cin abinci in ba bisa wasu dalilalai ba.

Abubuwan Da Ya Shafa: abinci ambata muminai ramadan
captcha