IQNA

Sharadin Saudiyya kan allurar alhazai

21:32 - May 08, 2022
Lambar Labari: 3487266
Tehran (IQNA) Ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanar da cewa, babban abin da ake bukata na yin rijistar maniyyatan bana shi ne a yi musu allurar rigakafin da Saudiyya ta amince da ita.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Arabiya cewa, ma’aikatar aikin Hajji ta kasar Saudiyya ta sanar a cikin wani sako cewa: Wajibi ne alhazan shekara ta 1443 bayan hijira su kammala allurar rigakafin cutar Korona ta hanyar yin daya daga cikin allurar da ma’aikatar lafiya ta kasar Saudiyya ta amince da su.

Ma'aikatar Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta kuma sanar da cewa, za a kammala aikin Umrah na masu zuwa daga kasashen waje da bizar Umrah a ranar 30 ga watan Shawwal (11 ga watan Yuni).

A shekarar bana dai Saudiyya ta bayar da izinin yin aikin hajji ga maniyyata miliyan guda, sabanin shekaru biyu da suka gabata da aka kayyade adadin da ‘yan dubban mutane saboda yaduwar cutar corona.

Koa  shekarar bana Saudiyya ta jaddada cewa koda maniyyata sun yi allurar rigakafi, dole ne su kiyaye ka’idiji na kiwon lafiya.

 

 

 

 

 

4055346

 

 

captcha