IQNA

Oman ba za ta kulla alakar da gwamnatin yahudawan sahyoniya ba

16:56 - May 28, 2022
Lambar Labari: 3487354
Tehran (IQNA) A ranar Asabar din nan ne ministan harkokin wajen kasar Omani ya bayyana rashin amincewar kasar na daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawan tare da yin kira da a warware matsalar Palastinu cikin adalci.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik Larabci ya nakalto Badar al-Busaidi ministan harkokin wajen kasar Oman yana cewa, kasarsa ita ce kasa ta farko ta larabawa da ke gabar tekun Farisa da ta goyi bayan zaman lafiya a Palastinu tun bayan yarjejeniyar Camp David a shekarar 1979.

Ya jaddada cewa Oman ba za ta shiga yarjejeniyar da ake kira yarjejeniyar Abraham ba domin daidaita alaka da gwamnatin yahudawan sahyoniyawa, domin kuwa sun fi fifita shirye-shiryen da ke tallafawa al'ummar Palastinu da kuma kare hakkokinsu.

Ministan harkokin wajen Omani ya bayyana cewa: Duk wata nasara da aka cimma a yarjejeniyar Abraham, dole ne ta kai ga warware matsalar Palasdinu ta karshe, mai dorewa da adalci bisa tsarin kasashe biyu.

A kwanakin baya ne dai Eliav Benjamin, shugaban sashin kula da zaman lafiya na ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila a gabas ta tsakiya ya ce Oman na iya zama kasa ta gaba da za ta daidaita alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Shafin yanar gizo na I24 ya nakalto Eliav yana cewa: "Bayan maraba da yarjejeniyar Abraham, gwamnatin sahyoniya  ko da yaushe tana bayyana kasar Oman a matsayin daya daga cikin kasashen da ke son kulla huldar jakadanci da Tel Aviv.

Benjamin ya kara da cewa: "Wannan gwamnatin tana tattaunawa da dukkan kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka. Za mu ci gaba da hadin gwiwarmu da masarautar Oman."

Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila a ranar 15 ga Satumba, 2020, sannan Sudan a ranar 23 ga Oktoba, 2020, sannan Maroko a ranar 10 ga Disamba, 2020, a karkashin matsin lambar Amurka da tsohon shugaban kasar Donald Trump.

 

4060271

 

captcha