Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Sabah, rundunar ‘yan sandan Karbala da ‘yan sandan wannan lardi a cikin wani cikakken shirin tsaro da suka gudanar, sun yi nazari kan shirye-shiryen farko na tsare-tsare na musamman na samar da tsaro ga miliyoyin maziyarta a wannan gari, da suka hada da tarukan Ashura a daidai lokacin da watan Muharram ke gabatowa.
Janar Ali al-Hashemi kwamandan ayyuka na Karbala ya sanar da cewa: Wannan taron na tsaro ya samu halartar manajojin tsaro da na leken asiri da kwamandoji da dimbin sojoji da jami'an 'yan sanda da wakilan haramin Hussaini da Abbasi da Al-Hashd al-Shaabi , ya yi nazari tare da bayyana ma'auni na shirin tsaro na musamman na Muharram, Kuma an rarraba ayyuka.
Al-Hashemi ya yi nuni da cewa, kwamandojin tsaro na musamman na Ashura sun shirya shirin tsaro: Tare da tsare-tsare na musamana bangaren kiwon lafiya.
Ya ce: Dukkan ma'aikatu da ma'aikatun gwamnati za su shiga cikin tsare-tsare na musamman na wannan taro da kuma yadda za a samu saukin shigar maziyarta zuwa Karbala da halartar tarukan cikin nasara.