IQNA

Wane ne ya kai wa Salman Rushdie hari?

16:37 - August 13, 2022
Lambar Labari: 3487681
Tehran (IQNA) Hukumomin jihar New York sun bayyana wani matashi dan shekara 24 mai suna "Hadi Matar" a matsayin wanda ya kai wa Salman Rushdie hari a jiya, inda suka ce maharin dan asalin jihar New Jersey ne.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharin a halin yanzu yana hannun jami’an ‘yan sandan jihar New York, yayin das hi kuma Rushdi yana kwance a asibiti.

Hukumar ‘yan sanda ta New York na kokarin samun takardar neman izinin binciken kadarorin da ke da alaka da Hadi Matar, don ci gaba da bincike kan lamarinsa, domin kuwa a cewar majiyoyin na Amurka, har yanzu ba a tuhumi Hadi Matar a hukumance ba a kan lamarin.

Wakilin Kamfanonin Dillancin Labarai sun ruwaito cewa, Salman Rushdie, wanda ya yi ridda daga addinin musulunci kuma mawallafin littafin ayoyin Shaidan, wanda ya ci zarafin Manzon Allah (SAW), an kai masa hari a lokacin da yake shirin gabatar da jawabi a birnin New York.

Binciken da 'yan jaridar ya yi na nuni da cewa wani mutum ne ya garzaya zuwa dandalin jawabin inda ya kai masa hari da wuka.

Lamarin ya faru ne da karfe 11 na safe agogon New York A cewar rahoton, an kai Salman Rushdie asibiti a jirgin sama mai saukar ungulu jim kadan bayan faruwar lamarin.

4077838

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha