Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Akhbar cewa, Youssef Belmahdi ministan kula da harkokin addini na kasar Aljeriya ya sanar da buga kur’ani mai tsarki bugu na farko da harshen makafi.
Belmahdi ya sanar a jiya Litinin 22 ga watan Maris cewa a karon farko a tarihin kasar Aljeriya an buga kur'ani mai tsarki kamar yadda ruwayar Varsh ta ruwaito kuma a cikin rubutun al'ada da kuma rubutun makafi a wannan kasa, kuma za a buga kwafi dubu biyar a farkon.
Belmehdi ya kara da cewa: Sabuwar fasahar makafi ta dogara ne akan rubuta kalmomi da rubutu na al'ada ta yadda iyaye za su iya raka 'ya'yansu masu karatu da rubutun makafi.
Ministan Aljeriya ya ce bisa ga umarnin shugaban kasar, za a aika wasu daga cikin wadannan kwafi dubu biyar zuwa kasashen Afirka da babban masallacin birnin Paris, sauran kuma za a raba su a cikin kasar.