Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, tare da daukar nauyi daga Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan, shugaban hadaddiyar daular larabawa tare da bin Mr. Sheikh Mansour Bin Zayed Al Nahyan mataimakin shugaban masarautar , Babban Sashen Kula da Harkokin Addinin Musulunci na kasar ya buga juzu'i na kur'ani kusan 100,000
Omar Habtoor al-Raei shugaban babban sashin kula da harkokin addinin muslunci da baiwa ya yi bayani game da kulawar Muhammad bin Zayed na musamman ga kur’ani da ilimi inda ya jaddada cewa yana tallafawa cibiyoyi masu alaka da kiyaye kur’ani mai tsarki ta hanya ta musamman. sannan kuma hanyar Sheikh Zayed bin Sultan Al Nahyan na ci gaba da gudana, wanda shi ne ya kafa cibiyar kur'ani mai tsarki ta Masarautar.
Al-Dara'i ya ce game da buga sabon tarin kur'ani: An gudanar da wannan tarin ne bisa tsarin aikin buga kur'ani da kuma kudin da shugaban kasa ya bayar, wanda ya sa ido a kan gudanar da wannan aiki.
A cewar Al-Daraei, za a raba wadannan kur’ani ne a masallatai da cibiyoyin haddar kur’ani da cibiyoyin bayar da agaji a ciki da wajen kasar UAE.