A yayin wannan ganawa, malamai da dama sun karanta ayoyin kur’ani mai tsarki da kuma Ayatullah Khamenei, yayin da yake nasiha ga masu karatun kur’ani da su isar da ma’anonin ayoyin da ake karantawa ga masu saurare, sun jaddada cewa: Karatun kur'ani kayan aiki ne, hanya ce; don me? Don samun ilimin kur'ani a cikin zuciya; Da farko dai ita ce raya al'ummar musulmi. A wajen taron da kuke karatun kur'ani, zai yi kyau bayan karantawa misali minti goma ko kwata, ku iya nuna jigogi na aya ga masu sauraron karatunku. Minti biyar ko minti goma sai ya fadi wadannan ayoyin da ya karanta, Wannan yana da kyau sosai; Wannan yana daga darajar masu sauraro, da majalisin kur’ani.
Jagoran Jyin Juya Halin Musulunci 28 April 2024