IQNA

A wajen kaddamar da littafin “Karatu a cikin Baha’iyya" :

A mahangar dukkan musulmi, Baha’iyya batattu ne

15:19 - May 18, 2024
Lambar Labari: 3491171
IQNA - Wani masani a a fagen sanin akidar Baha’iyya  ya ce: Akidar da dukkan musulmi Shi'a da Sunna suke da a dukkan kasashen duniya shi ne cewa Baha’iyya kafirai ne kuma suna kokarin yada al'adunsu a kasashen musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar baje kolin litattafai na kasa da kasa karo na 35 a  Tehran cewa, an kaddamar da littafin "Karatu a cikin akidun Baha’iyya " wanda Maryam Safiuddin ta fassara daga littafin "Qiraa fi watha’iq al-Baha'i" wanda " Ayesha Abdul Rahman" ta.

Abdul Hossein Fakhari, wanda ya kware a fannin karatun Baha’iyya, ya bayyana cewa Ayesha Abdul Rahman, wacce aka fi sani da "Bent Al-Shati", marubuciya c eta na littafin,  ɗaya ee daga cikin manyan masu sharhi da marubuta na Masar.

 Ya kara da cewa: "Bent al-Shati" na ganin cewa al'ummar Masar ba su san harkar Baha’iyya ba, don haka suna daukar wannan lamari a matsayin sabani kawai na fahimta.

Wannan farfesa na nazarin Baha’iyya ya ce game da muhimmancin Masar ga Baha’iyya: An tsawaita batun Baha’iyya a Masar saboda shari'o'i 2 na kotu da ma'aikatar tsaron Masar ta yi. Baha'is sun  yi imanin cewa amfani da Islama ya ƙare kuma Masar ta daɗe tana bin lamarin Baha’iyya .

 Game da Baha’iyya, Fakhari ya ce: A wata fatawa da aka yi shekaru da suka gabata, Baha’iyya ba ya cikin wata mazhabar Musulunci, kuma masu karkata zuwa ga Baha’iyya sun yi ridda, saboda warware abubuwa da suke a cikin musulunci, musamman manzancin manzon allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa.

 

4216420

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: manzon allah littafi imani addini musulunci
captcha