IQNA

Ganawar Ayatullah Yaqubi da Shaikh Zakzaky

15:29 - May 18, 2024
Lambar Labari: 3491172
IQNA - Shugaban Harka Islamiyya a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky ya da Ayatullah Yaqoubi, a birnin najaf Ashraf
Ganawar Ayatullah Yaqubi da Shaikh Zakzaky

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya Ayatullah Sheikh Muhammad Yaqoubi ya yi tsokaci kan kokari da kuma ayyukan ci gaba da wayar da kan jama’a domin isar da muryar Musulunci da kuma bayyana irin daukakar mazhabar Ahlul Baiti (a.s) da karfintaa kasashen duniya, kiyayewa da samar da mafita ga matsaloli da kalubale a gaban al'ummomin bil'adama da hadin kan musulmi.

Wadannan kalamai sun zo a lokacin wata ganawa da Ayatullahi Yaqoubi da Sheikh Ibrahim Zakzaky na Najeriya a ofishinsa da ke Najaf.

Ya yaba da abin day a kira hakuri da juriya irin na Sheikh Zakzaky kan abubuwan da suka faru   da shi, inda ya ce har kullum juriya wajen aikin addini lamari ne mai matukar tasiri wajen isar da sako.

Haka nan kuma ya bayyana ci gaba da ake samu wajen yaduwar fahimtar addini a Najeriya da sauran kasashen Afirka, da kuma bayyana hakan a matsayin wani babban sauyi na ci gaban musulunci.

 

Don haka ne Ayatullah Yaqoubi ya jaddada wajabcin hada karfi da karfe tsakanin dukkanin bangarori masu tasiri na addini wajen bayar da gudunmawarsu wajen dafawa masu isar da sakon addini a fadin nahiyar Afirka.

A karshe Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa ya kafa cibiyoyin bayar da agaji da dama domin samar da ayyuka daban-daban ga mabiya tafarkin Ahlul Baiti (a.s) kuma ayyukansa na farko fara ne tun shekaru 45 da suka gabata.

 

 

 

 

 

4216379

 

 

captcha