Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Khalij cewa, faifan bidiyon karatun ayoyi daga cikin suratul Mubaraka Fatir da wani matashin mai karatu daga kasar Saudiyya ya yi ya ja hankalin masu amfani da shafukan sada zumunta. An kalli wannan bidiyon fiye da miliyan 2 da sau dubu dari takwas tun lokacin da aka saki shi.
Wannan matashin mai karatu yana karanta wadannan ayoyi daga cikin suratul Fatir mai albarka.