IQNA

Shugaban Kasar Iran Da Tawagarsa Sun Yi Shahada

10:44 - May 20, 2024
Lambar Labari: 3491181
IQNA - Bayan gano jirgin mai saukar ungulu da ya fado, Ayatullah Sayyid Ibrahim Raisi, shugaban kasar Iran da tawagarsa sun yi shahada.

Bayan hatsarin da jirgin saman shugaban kasa da tawagarsa suka yi, da misalin karfe 5:30 na safiyar yau,  tawagar agaji ta Red Crescent ta yi nasarar gano inda hatsarin ya afku da jirgin.

Shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar Pir Hossein Koulivand ya tabbatar da wannan labari inda ya ce: Bayan gano jirgin mai saukar ungulu da ya fado, ba a samu alamun mutanen da ke cikin jirgin a raye ba.

Ya kamata a lura da cewa, yanayin  mai wahala ne, rashin isa wurin, hazo, sanyi da kuma ruwan sama, ya sa aka kasa gano inda hatsarin ya afku cikin sauki, kuma a saboda haka ne tawagar masu aikin ceto suka gudanar da aikin isa yankin a cikin wahala. Daga karshe dai an ci gaba da gudanar da bincike har zuwa safiyar yau.

Lokacin da aka gano tarkacen jirgin mai saukar ungulu, babu wani daga cikin wadanda suke cikin jirgin da ya tsira.

Tare da gano gawarwakin fasinjojin jirgin mai saukar ungulu dauke da shugaban kasar da tawagar da ke tare da shi kuma bisa ga bayanin da aka samu, Ayatullah Sayyid Ibrahim Raisi; Hossein Amirabdollahian; Ministan harkokin wajen kasar, Ayatollah Sayed Mohammad Ali Al-Hashem; Ilimamin Juma'a Tabriz kuma wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a lardin Azarbaijan ta gabas, da Malik Rahmati,  gwamnan Azarbaijan ta gabas, da sauran abokan tafiyarsu duk sun rasa rayukansu.

Idan dai ba a manta ba, a jiya 19 ga watan Mayu ne shugaban kasar da tawagarsa suka je birnin Khodafarin da ke kan iyaka, domin bude madatsar ruwa ta Qiz Qalasi, wani aikin samar da ruwan sha na hadin gwiwa tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Jamhuriyar Azarbaijan, da kuma kammala aikin. da fadada madatsar ruwa ta Khodaafrin A lokacin da suka koma Tabriz, wani jirgin sama mai saukar ungulu da ke dauke da su ya  yi hadari a kusa da birnin Varzeghan. 

 

 4216875

 

 

captcha