IQNA

Daga kafa / Sunnonin Ubangiji a cikin kur'ani 2

20:32 - August 24, 2024
Lambar Labari: 3491749
IQNA - A cikin al’amarin Alkur’ani, Istradaj yana daya daga cikin sunnar Allah wadanda ba su canzawa wadanda saboda sabon mutum da dagewar da yake yi da zunubi, sai a hankali hakan ya kai shi cikin ramin halaka da ramukan faduwa.

A cikin kur'ani mai girma Istdraj yana daga cikin sunnonin  Allah da ba za su iya canzawa wadanda saboda sabon mutum da dagewar da yake yi a kan zunubi, sai a hankali ya ja shi zuwa cikin ramin halaka da faduwa. Akwai misalai da dama kan a cikin ayoyi biyu na Alkur’ani: aya ta 182 a cikin suratul A’araf, sannan kuma  Aya ta 44 a cikin suratul Qalam.

Wadannan ayoyi suna nuna yadda mutum ke fadawa cikin tarko ta hanyar inkarin ayoyin Allah, kuma a hankali a hankali ya nutse a cikin zunubi da kuskure har ya kai matsayin da babu dawowa.

Ma’anar Istraji ta Kur’ani tana nuni ne da gangarowar mutane a hankali mataki-mataki zuwa inda za su nufa, ko kuma cudanya da rayuwarsu da dalilin rashin ambaton Allah. Wadanda kuma ba su yarda da kyakykyawan sakamako na shiriyar Allah ta asali da na shari’a da jarrabawa ba, a karshe Allah zai yi watsi da su gaba daya, kuma hatta wuraren faduwa da kaskancinsu a shirye suke, ta yadda za su kusance su, da Mummunan ƙarshensu, kuma ba zato ba tsammani zasu fada cikin azabar Allah.

Sunnar Istidraj tana da alamun da ya kamata a kula da su. Allah a bisa sunnarsa yana ba azzalumai dama su shirya kafin azabar lahira. Tabbas samun ni'ima ba azaba ba ce, amma yana bukatar godiya, idan kuma ba a yi godiya ba, Allah zai bar mutum shi kadai, ya yi masa azaba bisa ga kafice wa ni’ima da rashin yin amfani da ita ta hanyar da ta dace wajen biyayya ga dokokinsa.

Alamar azaba bisa sunnar Istadraj ita ce mutum ya gafala da Allah a cikin dukiyarsa ta duniya kuma ba ya aikata wani abu da ke nuna kasantuwar ruhi da Iblis a rayuwarsa,idan kuma ya yi mafani da wannan damar wajen yin godiya ga Allah da yin biyayya gare da barin sabonsa, to ba zai shiga cikin babin Istidraji ba.

 

3489586

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: dawowa biyayya ga Allah bauta ayoyi kur’ani
captcha