Shafin Al-Watan ya bayyana cewa, karatun kur’ani mai kayatarwa da wani masinja babur ya yi a cikin zirga-zirga a titunan birnin Landan ya samu karbuwa sosai daga masu amfani da shafukan sada zumunta.
A cikin wannan bidiyo yana karanta wadannan ayoyi na suratu Mubaraka Ahzab da nishadi.
A shekarun baya-bayan nan dai musulmi a kasar Ingila sun fuskanci matsalar kyamar addinin Islama da kuma hare-hare daga wasu masu ra'ayin rikau na kin jinin musulunci.