IQNA

Kakakin Hashd al-Shaabi:

Ba za a sake maimaita yanayin 2014 na ISIS a Iraki ba

13:55 - December 05, 2024
Lambar Labari: 3492326
IQNA - Kakakin rundunar "Hashd al-Shaabi" ya jaddada cikakken shirin sojojin Iraki na kare iyakokin kasar da sauran yankunan kasar, sannan ya jaddada cewa ba za a taba maimaita irin yanayin da kasar ta shiga a hannun 'yan ta'adda na ISIS a shekarar 2014 ba.

Shafin middle East ya bayar da rahoton cewa, rundunar Hashd al-Shaabi ta tabbatar wa al'ummar kasar cewa ba za a taba samun irin wannan yanayin na shekarar 2014 a kasar ba.

Moayed al-Saadi, kakakin dakarun  Hashd al-Shaabi, a wata hira da jaridar "Al-Sabah" ta kasar Iraki, a daidai lokacin da ake samun  saurin sauye-sauye cikin sauri a kasar Siriya, ya bayyana cewa: Dukkanin matakan da dakarun Hashd al-Shaabi suka dauka suna cikin tsarin shawarwarin Mohammad Shi'yaa Al-Sudani babban kwamandan sojojin kasar da kuma Faleh Al-Fayyad shugaban rundunar Popular Mobilisation Organisation, ko kuma Hashd al-Shaabi, inda suke magana  akan bukatar karfafa shingen kan iyaka na Iraki da Siriya don hana maimaita abin da ya faru a cikin 2014.

Dakarun sojin kasar Iraki da Hashd al-Shaabi, sun tabbatar da cewa yiwuwar faruwar irin wadannan al'amura ba abu ne da za a bari ba.

Kakakin Hashd al-Shaabi ya bayyana cewa: Manufar Tafiyar Falah al-Fayad shugaban wadannan dakaru zuwa lardin Nainawa a haƙiƙa ita ce don isar da saƙo mai ƙarfafawa ga Hashd al-Shaabi cewa dakarun sun shirya tsaf don tallafawa ƴancin kasar Iraki da shirye shiryen kasancewa a fagen daga  bisa ga umarnin babban kwamandan rundunar soji ta kasar Iraki.

 

 

4252395

 

 

 

 

 

captcha