Mministan aikin hajji da umrah na kasar Saudiyya Tawfiq Al-Rabiah ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata adadin mahajjata da aikin umrah ya kai mutane 18,535,689.
Al-Rabi'ah ya kara da cewa: Mutane miliyan 16,924,689 ne suka tafi kasar Saudiyya aikin Hajjin Umrah, yayin da mutane miliyan 1,611,310 suka tafi kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin Tamattu.
Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya ya ce adadin maniyyatan da suka je Masallacin Annabi (SAW) su ma sun kai fiye da miliyan 13 a shekarar 2024.