Shafin yanar gizo na “24saa.com” ya habarta cewa, ana gudanar da wannan gasa ne a daidai lokacin da ake gudanar da azumin watan Ramadan tare da hadin gwiwar ma’aikatar bayar da kyauta da harkokin addinin musulunci ta kasar Morocco.
Kamar yadda wani faifan talla da gidan talabijin na Morocco ya fitar, ya nuna cewa, gasar za ta kasu kashi biyu ne: ‘yan mata da maza, a tsakanin shekaru 10 zuwa 20, da nufin karfafa wa matasa kwarin gwiwa kan fasahar karatun kur’ani.
An fara rijistar ta hanyar dandali da aka kebe domin shiga wannan gasa, kuma a cewar sanarwar tashar talabijin ta Morocco 2, wannan gasar kur’ani wata dama ce ga mahalarta taron wajen nuna kwarewarsu ta karatun kur’ani tare da kiyaye ingantattun ka’idojin tajwidi.
Sanarwar wannan gasa ta samu kyakkyawar tarba daga masu amfani da shafukan sada zumunta, inda suka yi maraba da dawowar irin wadannan shirye-shirye, tare da sanar da cewa, wannan gasa ta kasance mai tunawa da tsohon gasar "karatu tare da kiyaye dokokin tajwidi" a gidan talabijin na Morocco.