Khalid bin Salman ministan tsaron kasar Saudiyya ya gabatar da sakon sarkin kasar ga Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a yammacin jiya Alhamis 2 ga wata a wata ganawa da jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada a cikin wannan ganawar cewa: Mun yi imani da cewa dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Saudiyya za ta kasance mai amfani ga kasashen biyu, kuma kasashen biyu za su iya taimakawa juna.
Yayin da yake jaddada cewa fadada alaka tsakanin kasashen biyu yana da makiya, Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wajibi ne a shawo kan wadannan dalilai na kiyayya, kuma a shirye muke kan hakan.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da wasu ci gaban da Iran ta samu, ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta taimaka wa Saudiyya a wadannan fagage.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Yana da kyau 'yan'uwa a wannan yanki su hada kai da taimakon juna fiye da dogaro da wasu.
A cikin wannan taro, wanda kuma ya samu halartar babban hafsan hafsoshin sojan kasar Manjo Janar Baqeri, ministan tsaron kasar Saudiyya Khalid bin Salman, ya bayyana matukar jin dadinsa da taron inda ya ce: Na zo Tehran ne da ajandar fadada alaka da Iran da hadin gwiwa a dukkan fannoni, muna fatan wannan tattaunawa mai ma'ana ta samar da kyakkyawar alaka tsakanin Saudiyya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran fiye da a baya.