Cibiyar bayar da agajin jin kai ta Turkiyya İHH ta kaddamar da wasu masallatai biyu da rijiyar ruwa a kasar Mali da ke yammacin Afirka yayin wani biki.
Gidauniyar ta sanar da cewa, an gina daya daga cikin wadannan masallatai tare da bude shi a yankin Balafinbogo mai tazarar kilomita 60 daga Bamako babban birnin kasar Mali, dayan kuma an gina shi tare da bude shi a yankin Falako mai tazarar kilomita 200 daga babban birnin kasar.
Haka kuma saboda bukatun yankin an haka rijiyar ruwa aka fara aiki tare da masallacin Falako.
Jami’ai da dama, da daraktocin wannan gidauniyar agaji ta Turkiyya, da mazauna yankin sun halarci bikin.
Jamhuriyar Mali kasa ce da ke yammacin Afirka kuma daya daga cikin manyan kasashen musulmi a nahiyar Afirka. Musulman kasar sun fi kashi 90 cikin 100 na al’ummar kasar, tare da sauran mazauna kasar da ke bin addinin na asali da kuma wasu Kiristoci.
Galibin musulmin kasar Mali mabiya Sunna ne kuma suna bin darikar Malikiyya. ‘Yan Shi’a na farko da suka zauna a wannan kasa ‘yan gudun hijira ne daga kasar Labanon.