IQNA

An Gudanar Da Makoki A Jajibar Ashura a Karbala

20:47 - July 06, 2025
Lambar Labari: 3493507
IQNA – Dubban daruruwan mutane ne suka hallara a birnin Karbala na kasar Iraki a jajibirin ranar Ashura domin tunawa da shahadar Imam Husaini (AS), a daya daga cikin manya-manyan bukukuwan addini na kalandar Musulunci.

Dimbin jama’a da suka fito daga sassan kasar Iraki da kuma kasashe da dama na duniya ne suka halarci zaman makokin da aka gudanar a hubbaren Imam Husaini (AS) da kuma dan uwansa Abbas bn Ali (AS) a Karbala a daren jiya Asabar.

Taron dai ya yi daidai da jajibirin Ashura, ranar 10 ga watan Muharram, wanda ke tunawa da shahadar Imam Husaini (AS) jikan Manzon Allah (SAW) da kuma sahabbansa a yakin Karbala a shekara ta 680 miladiyya.

Shagulgulan sun hada da kade-kaden makoki na gargajiya da na fitulu, yayin da mahalarta taron ke karrama shahidan filin Karbala.

“Daga cikin jama’a masu yawan gaske da mabiya Imam Husaini (AS) sun kunna fitulun tunawa da shahidan kasar Naynawa,” kamar yadda hukumar ta ruwaito, yayin da take ishara da sunan yankin Karbala na tarihi.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Iraki ta sanar a jiya Lahadi cewa sama da mahajjata miliyan 1.176 ne suka shiga kasar tun daga farkon watan Muharram. A wani taron manema labarai, Kanar Abbas al-Bahadli, kakakin ma'aikatar, ya kara da cewa sama da maziyarta miliyan 1 ne kuma suka tashi daga Iraki a cikin wannan lokaci.

Al-Bahadli ya bayyana cewa, a hukumance an yi wa mabambanta 833 rajista a Karbala domin gudanar da bukukuwan Ashura, ciki har da mabambanta 10 daga wajen kasar Iraki. Waɗannan cibiyoyi suna ba da ayyuka kamar abinci, ruwa, da wurin kwana ga masu ziyara.

 

 

4292810

 

 

captcha