Kwanakin baya ne aka gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta “Al-kawthar” ga matasa masu koyo a gundumar India da ke Karbala. Taron dai wani shiri ne da ake ci gaba da gudanarwa mai taken “Yaranmu, Ma’abota Karatunmu,” wanda majalisar ilimin kur’ani ta gidan ibada ke tallafawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Kafeel cewa, cibiyar kur’ani mai tsarki reshen Indiya tare da hadin gwiwar hubbaren Sayyid Muhammad bn Hamza (AS) ne suka shirya gasar karo na uku a jere.
Yara 18 ne suka halarci gasar. An fara taron ne da karantawa daga bakin Mustafa Raheem daya daga cikin wadanda suka halarci taron.
A yayin bikin, Karim al-Hindawi, mai karatun kur’ani kuma wakilin hubbaren Sayyid Muhammad bn Hamza ya gabatar da jawabi ga mahalarta taron. Ya kuma ja hankalin yaran da su shiga cikin shirye-shiryen kur’ani da zurfafa alakarsu da nassi mai tsarki.
A karshen gasar, an zabi yara shida a matsayin wadanda suka yi fice a gasar. Dukkanin mahalarta taron sun samu kyautuka bisa la'akari da kokarin da suka yi.