IQNA

Karatun Qasem Moghadadi a Karbala

17:35 - August 24, 2025
Lambar Labari: 3493763
IQNA - Qasem Moghadadi, makarancin kasar Iran, ya gabatar da karatun kur’ani a cikin ayarin Arba’in ta hanyar tattakin Arba’in da kuma jerin gwano da dama, ciki har da hubbaren Imam Husaini (AS).

Ayarin Arba'in mai suna "Imam Ridha (AS)" sun kasance suna gudanar da tattakin Arba'in inda suka aike da malamai da makaranta sama da 80, daga cikinsu akwai malamai daga kasashe 13 daban-daban.

Daya daga cikin makarantun da suka halarci wannan ayari shine Qasem Moghadadi, makarancin kasa da kasa n wanda ya gabatar da jerin karatuttuka  daban-daban.

Bayan shi, Muhammad Hossein Farahani, mai karatu kuma liman na hubbaren  Sayyida  Masoumeh (AS) da kuma masallacin Juma'a na Jamkaran, shi ma ya karanta kur'ani a cikin wadannan jerin gwanon.

Yana da kyau a lura cewa ayarin kur'ani na Arba'in ya kasance a hanyar tattakin Arba'in Hussain daga Najaf Ashraf zuwa Karbala.

 

 

 

 

4301263

 

 

captcha